Fitattun ‘yan Jarida zasu halarci taron bikin bada kyaututtuka da karramawa wanda Kwamitin Kare ‘Yan Jarida ke shiryawa a duk shekara don bikin ‘yancin ‘yan jarida a yanayin da duniya ke ciki na rashin kwanciyar hankali

Fitacciyar jarumar fina-finai Meryl Streep za ta karrama Lauya Amal Clooney da kyautar ‘yan cin ‘yan jarida na  ‘CPJ Gwen ifill’

Za a nuna wannan biki na bada kyaututtu kai tsaye ta hanyar yanar gizo a tashoshin NBC, CBS da ABC ranar 19 ga Nuwamba da misalin karfe 8 na dare. EST.

Domin karrama kwarewa da jarumta na ‘yan jarida, Kwamitin Kare ‘Yan jarida zai karrama wasu fitattun ‘yan jarida da suka nuna jarumta da jajircewa a lokacin aikin jarida su hudu daga kasashen Bangaledesh, Iran, Najeriya da Rasha, wanda dukkan su mahukunta a kasashen su sun taba tsare su kuma an muzguna musu ta hanyoyi da dama a dalilin aikin su na dauko labarai, wato aikin jarida.

Bikin karrama ‘yan jarida na shekarar  2020 na nuna sadaukarwar da kungiyar ke yi wajen  kare ‘yancin’ ‘yan jarida a ko ina a fadin duniya.

Za a karrama lauya kuma mai kare hakkin Dan Adam Amal Clooney da kyautar Gwen Ifill ta 2020 wanda jarumar fina-finai Meryl Streep, da ta yi fice wajen nuna goyon bayan ta ga ‘yancin ‘yan jarida. A wannan kasaitaccen buki wanda za a yada shi ta yanar gizo, za a nuna bidiyon ayyukan wadanda za a karrama wanda duk an taba saka su a wasu kafafen yada labarai a baya.

“ A irin wannan lokaci na zaman dar-dar, ba a san me zai faru yanzu-yanzu ba, ‘yan jarida ne ke waje a cikin wannan yanayi , suna kokarin dauko mana gaskiyar abinda ke faruwa sannan su bamu ta yadda zamu fahimci labarin ba tare da mu mun wahala ba,muna zaune. Suna yin haka ta hanyar yin tambayoyi mazu zurfi sannan kuma da bin diddigin gaskiyar magana ta kowani hali. Wadannan mutane ne masu muhimmancin gaske sannan suna bada gudunmawar su wajen yi wa mutane dawainiya  da kuma kare dimokradiya. “ Inji Streep. “ A dalilin haka nake matukar farin cikin kasancewar ina daga cikin wadanda za su halarci taron bikin na wannan shekara.” Sannan kuma da ci gaba da mara wa Kwamitin Kare ‘Yan Jarida baya domin samun nasara a abubuwan da ta saka a gaba na aikin Kare ‘Yan Jarida.

Fitaccen mai shiryawa kuma mai gabatar da shirin labarai na tashar ‘NBC Nightly News’ Lester Holt ne zai jagoranci shirin wanda za a yada ta yanar gizo a shafin www.ipfa2020.org, sannan kuma za a yada a tashoshin labarai na NBC, CBS da na ABC ranar 19 ga Nuwamba da karfe 8 na yamma. EST.

Domin nuna goyon bayan su ga aikin jarida, tare da Holt wanda shine zai jagoranci shirin, fitacciyar ‘yar jarida na CNN, Christiane Amanpour, mai shirya shirin “Face The Nation” a tashan CBS, Margaret Brennan, Wakilin PSB a fadar gwamnatin Amurka, wato White House, Yamiche Alcindor da mai shirya shirin “World News Tonight” a tashar ABC David Munir da sauransu duk za su halarci taron.

Bayan haka kuma bikin zai amsa kiraye  da za a yi na nuna goyon bayan ‘yancin ‘yan jarida  ta yanar gizo da wayar tarho daga wasu manya a ciki da wajen aikin jarida da suka hada da jarumin fina-finai Rosamund Pike, Mai shirya shirin labaran Satirica News, Samantha Bee, Dan jarida Ronan Farrow da tsohon shugaban kungiyar ‘Yan jarida na kasashen duniya reshen Hollywood, Meher Tatna.

CPJ zai karrama wasu fitattu da aka yi gwagwarmaya da su a harkar aikin jarida hudu:

1 – Za a karrama dan jarida mai daukan hoto Shahidul Alam, dan kasar Bangladesh, wanda aka garkame a kurkuku a lokacin  aikin dauko labarai a 2017.

2 – Dan jarida mai zaman kansa, dan kasar Iran, Mohamed Mosaed, wanda a kwanakin nan ba da dadewa ba aka yanke masa hukuncin zama gidan Kaso na tsawon shekaru hudu sannan kuma aka hana shi aiki jarida.

3 – Za a karrama mawallafin Jaridar PREMIUM TIMES a Najeriya, Dapo Olorunyomi kuma gogarman tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida da aikin jarida.

4 – Svetlana Prokopyeva, Wakiliyar gidan Radiyon ‘FreeEurope/Radiyo Liberty dake kasar Rasha, wanda ita ma an  gurfanar da ita bisa laifin wai tana goyon bayan ta’addancin dalilin  wani sharhi da tayi a shirin gidan Radiyon.

 “ Wannan annoba ta zama babban kalubale ga ‘yan jarida a duniya, amma muna farin cikin samun lokaci da muka yi da zamu hadu don yin bikin murnar bajintar su. Wadanda za a karrama sun nuna kwazo, jajircewa da bajinta a wajen kawo mana labarai, Ina matukar bugun kirji da su da irin ayyukan da suka yi.” Inji Joel Simon, Babban directan CPJ

“ Duk da cewa za a yi bikin ne ta yanar gizo wanda hakan sabon abu ne a wurin mu, muna farinciki da murnar haka a kan damar da wanna kafa ya bamu domin bada labarai da dama a wajen bikin.

CPJ na karrama wasu zababbun mutane ne da kyautar ‘Gwen Ifill Press Award’ da suka jajirce wajen yin kira da tsayawa tsayin daka don tabbatar da  ‘yancin aikin jarida a duniya. Wanda za a karrama da wannan Kyauta a bana, Amal Clooney tayi fice wajen yin kira ga shugabannin kasashen duniya su rika tsaya wa tsayin daka domin kare  ‘yan jarida da karrama aikin jarida.

Ta rika shiga gaba don kare ‘yan jarida a matsayin lauyar su a lokacin da ake tsangwamar su ko neman a tozarsu akan aikin su sannan kuma a yanzu ita ce ke wakiltar fitacciyar ‘yan jarida  wanda aka karrama da kyartar Gwen Ifil na 2018 – Maria Ressa

An rika muzguna wa Ressa a kasar ta, ta Philippines saboda gidan radiyon da take aiki Rappler ya yada labaran yadda almundahana da cin rashawa yayi katutu a gwamnatin kasar ta.

Za ta hira da Clooney a matsayin wani bangare na bikin.

Shugaban gidaudiyar ‘Open Society, Patrick Gaspard’ ne zai shugabanci bikin na wannan shekara .

Domin Karin bayani game bikin da za ayi ta yanar gizo, kira  Kamfanin shirya taruka na Buckey Hall Events a (914) 579-1000 ko kuma ka kira ofishin CPJ a lambar waya kamar haka (212) 300-9021, za ka kuma iya aikawa da sako ta yanar gizo a wannan adireshi CPJdinner@buckleyhallevents.com.

‘Yan jaridar da gidajen Jaridu da ke so su yi hira da wadanda za a karrama  ko kuma wani jigo a Kwamitin Kare ‘Yan Jarida , CPJ zai iya aika wa da sako ta adireshin mu kamar haka press@cpj.org.

Game da Kwamitin Kare ‘Yan Jarida

Kwamitin Kare ‘Yan Jarida Kungiya ce mai zaman kanta wanda aikin sa shine kare hakkin ‘yan jarida a duk inda suke a fadin duniya. Muna kare ‘yan jarida  da basu kariya da damar dauko labarai ba tare da tsoron tsangwama ba  ko kuma a yi musu barazana a lokacin aikin su.