Yawan ‘yan jaridar da aka daure a kasashen duniya ya yi tashin gwauron zabi a shekarar 2022 fiye da shekarun baya. A cikin wannan shekara da aka yi fama da tashe-tashen hankula, matsi, shugabannin masu mulkin kama karya sun kara kaimi wajen muzgunawa kafafen yada labarai masu zaman kansu ta hanyar amfani da karfin mulki wajen dakile su da hana su bayyana ra’ayoyin su da karfin tsiya da kuma yi wa ‘yancin ‘yan jarida katangar karfe.
An buga a ranar Disamba 14,2022
Daga Arlene Getz/CPJ Babban Darakta
GAGGAN MASU LAIFI – INDA AKA FI CIN ZARAFIN ‘YAN JARIDA | TAUYE ‘YANCI DA HAKKI – YADDA AKA SAMU A NAHIYOYI DA SASSAN DUNIYA | HANYOYIN DA AKA BI WAJEN AIKIN WANNAN KIDIDDIGA ( KIDAYA)
A wannan shekara an samu karuwa matuka fiye da shekarun baya a yawan ‘yan jaridan da aka daure a dalilin aikin su a fadin kasashen duniya. A rahoton Kidaya na Kididdigar gidan yari na shekara-shekara da kwamitin Kare Hakkin ‘Yan jarida CPJ ya yi ya gano cewa akwai yan jarida akalla 363 da ke daure aka tauye musu ‘yancinsu zuwa 1 ga Disambar 2022. Wannan adadi ya zarce yawan wanda aka samu a shekarar bara da kashi 20 cikin 100 da ke nuna irin matsi da cin zarafin harkar aikin jarida da aka samu a wannan shekara.
A wannan shekara kasashen da su ka fi yawan ‘yan jaridan da aka muzgunawa, a tauye ya ‘yanci sannan kuma aka daure su sun hada da Iran, China, Myanmar, Turkey da Belarus. Duk wadannan matsaloli sun samo asali ne ta hanyar mulkin kama karya da ake yi a kasashen da kuma ganin ko ta halin kaka an murkushe harkar aikin jarida, sannan kuma ga fama da aka yi da irin matsalolin da aka samu sanadiyyar annobar Korona (COVID-19) sannan kuma da rugujewar tattalin arziki da aka samu a dalilin rikicin Rasha da kasar Ukraine.
A Iran, ‘yan jarida da dama na daga cikin Iraniyawa 14,000 da aka kiyasce an kama a lokacin murkushe zanga-zangar da mutane suka yi kan mutuwar Mahsa Amini, dake tsare a hannun ‘yan sanda a lokacin wacce Ba Kurdaciya ce mai shekaru 22 da aka kama bisa zargin karya dokar hijabi ta Iran.
Tun a watan Satumba, zanga-zangar ta bazu a duk fadin kasar, inda masu zanga-zangar ke kira da a baiwa mata ‘yanci sannan kuma da yin kira da a fara yajin aiki a fadin kasar kuma a hambarar da shugabanni kasar Iran.
Mahukunta sun tsare ‘yan jarida mata 22 cikin 49 da aka kama tun lokacin da aka fara zanga-zangar da hakan ke nuni da cewa lallai mata sun taka rawar gani wajen dauko rahotonni game da wannan zanga-zanga wanda mata ne ke kan gaba.
A kasar China kuwa, mahukunta sun tsaurara matakai ne akan tace labarai a yanar gizo a lokacin da aka fito yin zanga-zangar nuna kin amincewa da sabuwar dokar Kulle ta Korona (COVID-19), a dalilin haka an buga cewa an tsare ‘yan jarida masu yawa na dan wani lokaci yayin da suke dauko rahotanni game da wannan zanga-zanga.
Bayanan kididdigar Kidaya da CPJ ya fidda mai take kamar haka: Yadda ake ci gaba da yi wa marasa galihu da tsiraru fin karfi da danniya
‘Yan kabilar Kurdawa ne suka zama cikin matsi da muzgunawar gwamnatin Iran a dalilin harehare da suka yi kama da maida martani da gwamnati ta kai wa masu zanga-zanga, kuma akwai akalla ‘yan jarida ‘yan asalin kabilar Kurdawa 9 da ke tsare a gidan yari. A kasar Turkiyya, mahukunta sun tsare ‘yan jarida 25 wanda ‘yan asalin kabilar Kurdawa ne da ke aiki a kamfanin Dillancin Labarai na Mezopotamya, da kuma Jaridar JINNEWS wanda na mata ne zalla ko kuma wasu kamfanonin da suka yi amfani da rahotanni da kamfanonin jarida mallakin kurdawa dake yankin kasashen turai.
A kasar Iraqi kuwa duka ‘yan jarida uku da aka daure a kurkuku, bisa bayannan tantance yawan wadanda aka tsare da muka yi an daure su ne a kurkukun kudistan dake kasar Iraqi. Sannan kuma a kasar China mafi yawan ‘yan jaridan da aka daure ‘yan kabilar Uighurs ne daga Xinjiang, yankin da ake zargin Beijin da cin zarafi, danniya, muzgunawa da tauye musu hakkunan su sannan da daure daruruwan su bayan tauye musu ‘yanci saboda kasancewar mafiyan kabilun su musulmai ne.
Garkame ‘yan jarida a kurkuku hanya ce ta yadda shugabanni masu yin mulkin kama karya ke amfani da wajen dakile yancin ‘yan jarida. A kasashen duniya gwamnatoci na yin amfani da hanyoyi kamar kirkiro da “dokokin dakile labaran karya”, suna amfani da hanyoyi na bata mutum da kuma dokoki kawai don su nuna batanci ga aikin jarida suna kauce wa dokokin kasa sannan suna yi wa tsarin shari’a cin fuska sannan kuma suna amfani da fasahar zamani wajen leken asirin ga ‘yan jarida da iyalan su.
A kasashen kamar su Rasha zuwa Nicaragua zuwa Afghanistan, gidajen jaridu masu zaman kansu tuni an fatattake su saboda dokokin da zai hanasu aiki yadda ya kamata. Tuni ‘yan jarida suka yi gudun neman mafaka da tsira ko kuma a hana shi aiki da tsinana komai. Sai dai kuma duk da cewa matakan da ake dauka don a cin mutuncin ‘yan jarida na banbanta daga kasa zuwa kasa, wadanda muka tattara a wannan rahoto na CPJ wanda ya bada kididdiga da bayanai kan irin abubuwan dake faruwa ya fayyace yadda mahukunta ke amfani da karfin mulki da iko wajen aikata zalunci da yin ramuwar gayya.
A kasashe kamar su China da Saudi Arabiyya, su kan cigaba da tsare ‘yan jarida a gidan yari ko da bayan wa’adin zaman su a tsare ya cika. Wasu kuma za su rika yi musu rashin mutunci da nuna halin ko in kula. Misali a kasar Vietnam, ‘yar jarida Pham Doan Trang da aka daure ta na tsawon shekaru 9 saboda ta yada wasu rahotanni na adawa ga gwamnati , an dauke ta daga cikin gari Hanoi zuwa wani kauye dake da nisan Mil 900 nesa da yan’uwan ta, kawai dabarar haka don kada su iya rika kawo mata ziyara.
A kasar Belarus kuwa, wakiliyar gidan talabijin din Belsat, Katsiaryna Andreyeva daya daga cikin ‘yan jarida da yawa da aka kama sannan kuma aka tsare saboda kawai sun yada zanga-zangar da aka yi a kasar don adawa da shugaban kasar Aleksandr Lukashenko, ta kusa kamala wa’adin da aka dibar mata na zaman gidan yari sai kotu ta kara aika ta gidan yari na tsawon shekaru 8 wannan karo wai an same ta da laifin “yada bayannan sirri na kasar”
A kasar Turkiyya kuwa bayan kotu ta yanke hukuncin a sake shari’ar Hatice Duman , shekaru 20 bayan an yanke mata hukuncin rai-da rai, ‘yar jaridan ta shaida wa wata kotu a Instabul a cikin wannan watan cewa jami’an hukumar gidajen yarin kasar sun lalata mata takardun shari’ar da take da su don kare kanta makonni kafin a yi zaman shari’ar, da hakan tauye mata hakki ne na ta shirya wa shari’ar don kare kanta. ( Kafin nan, Duman ta shaida wa CPJ a hira da aka yi da ita cewa an kwashe mata kayan aiki da ma wadanda ba na aiki ba a samame da aka kai mata, cewa an kwashe littafan ta, teburinta na aiki kai har ma da fararen takardu da bata yi rututu akai ba duk an tattara an tafi da su.
Sauran mahimman abubuwa:
GAGGAN MASU LAIFI – INDA AKA FI CIN ZARAFIN ‘YAN JARIDA
#1: IRAN
Mahukunta a kasar Iran sun tarwatsa zanga-zangar da mutane suka fito yi saboda mutuwar Amini, wanda a dalilin haka an daure ‘yan jarida akalla 62 angarkame su a gidan yari ranar 1 ga Disemba. Da yawan ‘yan jaridar da aka tsare sun fi haka ba dun an saki wasu ‘yan jarida 21 bayan an bada belin su kafin a tattara wannan rahoto da kididdiga.
Adadin yawan mata da aka tsare bashi misaltuwa. A lokacin da kasar Iran ta yi gagarimin tsare ‘yan jarida a shekarar da aka samu tashin hankali a adalilin rashin amincewa da zaben shugaban kasa a 2009, akalla ‘yan jarida 47 ne aka tsare a 2012, 4 ne kawai cikin su mata.
A bayanan kididdigar da muka yi akwai mata 24 da aka lissafo su a cikin wannan rahoto; 22 daga cikin su an kama su kuma an tsare bayan an soma zanga-zangar.
A lokacin da ake yi wa ‘yan jarida kame a wannan shekara, majiya ta sanarwa CPJ yadda ake yi wa ‘yan jarida dirar mikiya tun da asuba, wato sanyin safiya a gidajen, tare da ‘yan sanda suna bi suna kwace musu wayoyi da kayan aiki sannan su lakada wa wadanda suka tsare a wurin su dukan tsiya.
Akwana a tashi za a daina jin duriyar su, shafukan su ta sada zumunta a yanar gizo shima za su daina aiki, wanda shine hanyar da suke watsa labarai wanda dama can gwamnatin kasar ta saka doka akai duk za a daina ganin su. Kodai gwamnati ta rufe su, ko kuma wasu ‘yan jaridar su daina amfani da shafukan wato su goge su gudun kada gwamnati ta kawo musu farmaki saboda labaran da suke yi.
Mutum 62 da ke tsare a gidajen yari a akasar Iran shine adadi mafi yawa da CPJ ta samu a tsawon shekaru 30 da ya yi ya na yin irin wannan kididdiga duk shekara irin haka. Da hakan ya zarce yawan adadin wadanda aka samu bayan tashin hankalin da aka yi a kasar bayan zaben 2009.
#2: CHINA
Tsananin bincike da tantance komai da kasar China ke yi da kuma tsoron yin magana a cikin kasar da ke tsananta sa ido kan al’ummarta, ya sa yana da wahalar gaske musamman wajen gudanar da bincike kan sanin hakikanin adadin ‘yan jarida dake daure a gidajen yarin kasar.
A dalilin haka yasa za a ga an samu raguwa a yawan wadanda ke daure a gidajen yari saboda ba a san ainihin ko ‘yan jarida nawa ne ke tsare ba, Saboda haka za a ga daga yawan mutum 48 da aka samu a 2021 yanzu an samu mutum 43 ne a 2022. Dalilin haka ba zai sa a ce wai an samu ci gaba bane tunda yawan adadin ya ragu, kada a ga kamar cewa an samu sauki ne da ga matsi da muzgunawa aikin dauko labarai daga kamfanonin jarida masu zaman kansu.
‘Yan jaridar da ke yankin Uighur ne suka fi fuskantar matsi da tsananin horo akan abinda bai taka kara ya karye ba.Misali Omerjan Hasan na tsare a kurkuku na tsawon shekaru 15 saboda ya buga labarin tarihin lardin Xinjiang da aka ce wai gwamnati bata bashi damar haka ba.
Su kuwa Ilham Weli, Juret Haji, Mentimin Obul,da Mirkamil Ablimit an tsare su ne tun a shekarar 2018 wai ana zarginsu da wai yin fuska biyu, wata hanya da gwamnatin China ke amfani da shi suna tsare wasu wai dake nuna a fili suna tare da gwamnati amma a boye suna yake da manufofin gwamnati.
An daure wani Edita mai suna Memetian Abliz Boriyar tun a shekarar 2018, an daure shi ne bi sa laifin bada umarnin a saki wani lattafi wanda daga baya gwamnatin China ta haramta shi. Haka kuma wani abun tashin hankali shine locacin da wasu dalibai da suka yi wa Ilham Tohti aiki, dan jaridar da aka yanke wa hukuncin rai-da-rai, wanda shine mawallafin Jaridar Labarun Xinjiang a yanar gizo Uighurbiz, wadannan dalibai na daga cikin wadanda ake zaton sun kamala wa’aadin zaman su a gidan yari, sannan sai aka kaisu wani sansani na horaswa maimakon tunda sun kamala wa’adin zaman su a sake su kawai.
A Hong Kong an tabbatar gidajen jaridu masu zaman kansu ba su iya yin komai a dalilin bita da kullin da gwamnatin China, wato Beijing ke yi kamar irin kamfanonin na hamshakin dan kasuwa mai rajin kare dimokuradiyya Jimmy Lai. Tsare Lai da aka yi tun 2020, nuni ne na yadda gwamnati ke cigaba da adawa da kyamatar a bin yadda doka ta tsara da kuma tsarin da aka amince da shi na “kasa daya, tsarin mulki biyu” da ya baiwa kasar Hong Kong yanci a tsarin mulki da shari’a daga China. Ana cigaba da tsare Lai a kurkuku duk da ya kamala wa’adin watanni 20 din da aka yanke masa kan laifuka dabandaban. Ranar 10 ga Disamba, a daidai yana sauraren wata shari’ar da za ayi akan sa da zai iya sa aka yanke masa daurin rai da rai karkashin dokar karfakarfa na tsaron kasa , sai aka sake daure shin a shekaru biyar da wata tara bisa zargin Zamba da aka yi masa. Duk da cewa gwamnatin Hong Kong ta birkita masa shirin fuskantar shari’ar da yayi sabani da hukuncin da aka yanke a watan Nuwamba wanda babbar kotu ta yanke, wanda lauya daga kasar Birtaniya zai kare shi a shari’ar.
#3: MYANMAR
Kasar Myanmar ta haura can sama inda ta zama kasa ta biyu a cikin jerin kasashen da sakamakon kididdigar CPJ ya nuna da aka fi garkame ‘yan jarida a gidajen yari a cikin shekarar 2021, tun bayan hambarar da zababbiyar gwamnati da sojojin kasar suka yi sannan kuma da hana yada labarai kan sabuwar gwamnati da mahukunta suka yi.
Kamar yadda kungiyar kare hakkin dan Adam na Assistance Association for Political Prisoners, ta bayyana, wannan rikici da aka yi ya yi sanadiyyar mutuwan akalla mutum 2500 sannan kuma an daure mutane sama da 16,000 bisa zargin laifuka da suka jibanci siyasa.
Adadin yawan ‘yan jaridan da da aka daure a zuwa 1 ga Disamba ya kai mutum 42 daga mutum 30 da aka daure a 2021 a kokarin da kasar ke yi na ganin ta rufe bakunan ‘yan jarida da sauran gidajen yada labarai masu zaman kansu na kasar da suka rage. Da yawa daga cikin gidajen yada labarai na tsoron fadin matan su da wadanda ke aikin kansu bias tsoron matsanancin horo da muzgunawa da ake yi wa ‘yan jaridan.
Kusan rabin wadanda aka tsare and yanke musu hukunci ne a 2022, bisa wata dokar kasa da dake hukunta duk wanda ya ruruta wutar ingiza fitina da kuma yada labaran karya. A wani shari’ar kuma a watan Nuwamba an yanke wa dan jarida Myo San Soe hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari, bisa laifin zargin ta’addanci saboda tuntubar ‘yan kungiyar ‘People’s Defence Forces, wanda bangare ne na kungiyar gurguzu dake yaki da adawa da gwamanti mai ci.
#4: TURKEY
Adadin ‘yan jaridan da ake tsare da su a Turkiyya ya karu daga 18 a shekarar 2021 zuwa 40 a shekarar 2022 bayan da aka kama wasu ‘yan jaridar Kurdawa 25 a tsakanin tsakiya zuwa karshen shekara. Lauyan dake kare wadannan ‘yan jarida ya shaida wa CPJ an daure dukkan su bisa zargin aikata ta’addanci. Hanya da gwamnati ke amfani da shi wajen rufe bakin duk wadanda ke da alaka da haramtacciyar kungiyar Kurdawa wato Kurdistan Workers Party (PKK).
Sai dai kuma duk da cewa an samu karuwar ‘yan jarida da aka tsare a kididdigar bana, a kasar basu da yawa kamar yawan da aka samu sakamaon yunkurin juyin mulki da aka yi a kasar a 2016. Kafofin yada labarai masu zaman kansu na Turkiyya na ci gaba da tsukewa sakamakon garkame su da kwace su da kuma tilasta wa dimbin ‘yan jarida gudun hijira ko kuma ma su hakura da sana’ar kwatakwata.
Mutane da yawa a yanzu suna fargabar cewa kame da ake yi na baya-bayan nan alama ce ta akwai wata kullalliyar shiri na sake dakile ‘yancin ‘yan jarida gabanin zaben shekara mai zuwa, musamman ganin yadda majalisar dokokin Turkiyya ta amince da wata doka da ke cike da rudani kan kafafen yada labarai da zai tilasta duk wani da aka samu yana yada labaran da ba haka ba.
#5: BELARUS
A kasar Belarus kuwa, an tsare ‘yan jarida 26 ne zuwa 1 ga Disamba, da hakan karuwa ne aka samu daga mutum 19 da aka tsare a shekarar bara. Kusan rabin wadanda aka tsare ba a yanke musu hukunci ba, mutum biyu kuma na daure za su shafe shekaru 10 ko ma fiye a gidan yari.
Dukkan tuhume-tuhumen da ake yi musu sun hada da ko dai na ramuwar gayya ne ko kuma na adawa da kasa, kamar cin amanar kasa.
Tsare mutane da aka yi ya auku ne don ayi labule ga ci gaba da kokarin wanke Lukashenko domin a nuna wa mutane ba haka bane rahotannin da ake bugawa game da zaben sa da ke cika da rudani a 2020. Cikin wadanda har yanzu suna tsare akwai dan jarida Raman Pratasevich, wanda kama shi da aka yi ya jawo suka daga kasashen duniya bayan mahukuntan Belarus sun karkatar da jirgin saman fasinjoji da ya taso daga Lithuania zuwa babban birnin Kasar, Minsk, kawai domin su kama shi.
TAUYE ‘YANCI DA HAKKI – YADDA AKA SAMU A NAHIYOYI DA SASSAN DUNIYA
ASIA
Tauye hakki, cin mutunci da muzguna wa ‘yan jarida da kafafen yada labarai a kasashen China, Myanmar da Vietnam ya sa yankin Asia ke kan gaba waje yawan ‘yan jaridan da aka daure da suka kai mutum 119.
Vietnam dake da mutum 21, na nuna halin ko in kula ga aikin jarida musamman masu zaman kan su. Domin kuwa ba bu sassauci wajen daure duk wanda ya saba wa dokokin aikin jarida a kasar ta hanyar hukunci mai tsanani. A watan Oktoba, an daure Le Manh Ha tsawon shekara takwas a gidan yari, da bayan haka kuma zai yi zaman kulle a gida na tsawon shekaru biyar; A watan Agusta kuma an daure Le Anh Hung na tsawon shekaru biyar bisa laifin “ karya dokar kasa na yancin dimokradiyya ya amfani da yaka ya keta wa gwamnati, kungiyoyi da mutane rashin mutunci.”
Daga cikin wadanda ake tsare da su akwai Pham Doan Trang, wanda ya lashe lambar yabo ta CPJ ta kasa da kasa na ‘Yancin Jarida ta duniya a shekarar 2022. Trang na zaman daurin shekara tara a gidan yari a karkashin wata doka da ta haramta yada labarai ko yada labaran karya game da kasar.
Indiya, wacce ke da ‘yan jarida bakwai tsare a gidan yari, na ci gaba da shan suka kan yadda take mu’amala da kafafen yada labarai, musamman yadda ta yi amfani da dokar kare lafiyar jama’a ta Jammu da Kashmir, dokar hana tsarewa, don ci gaba da tsare ‘yan jaridar Kashmir da suka hada da Aasif Sultan, Fahad Shah, da Sajad Gul a gidan yari bayan kotu ta bayar da belinsu a wasu kararraki daban-daban.
Afganistan, mai ‘yan jarida uku da aka daure, ta fito a rahoton kidayar CPJ a karon farko cikin shekaru 12. Daruruwan ‘yan jaridun Afganistan sun tsere daga kasar bayan Taliban sun karbe ikon kasar a watan Agustan 2021; wadanda suka tsaya basu tsers ba sun fuskanci matsi domin do bi tsarin mulkin da sabuwar gwamnatin Taliban ta zo dashi bayan ta kafa gwamnati.
YANKIN KUDU DA SAHARA – AFIRKA
Yawan wadanda ke garkame a gidajen yari a yankin Afrika na bada bayanan da ba haka ba game da ‘yan cin ‘yan jarida. Kasar Eritrea ce ke kan gaba wajen daure ‘yan jarida, wacce it ace ta tara a duniya. Mutum 16 na tsare yanzu haka a gidajen yarin kasar ba tare da an yi musu shari’a ba ko samun damar zuwa ga iyalansu ko lauyoyinsu na tsawon shekaru 17 zuwa 22.
Kasar Kamaru kuwa na fitowa a jadawalin rahoton kidayar wadanda ke tsare a gidajen yari tun daga 2014. Kasar ce ta biyu da ta fi muni a yawan ‘yan jarida da aka tsare a nahiyar. Da ke da mutum biyar da ke garkame a kurkuku, a karkashin gurguwar tsarin shari’a wanda ya hada da amfani da kotunan soji wajen gurfanar da ‘yan jarida, wadanda su kuwa fararen hula ne karkashin dokokin kasa da kasa.
Ethiopia, wacce ta ke biye da kasar Eritrea a bara a matsayin kasa da daure ‘yan jarida ya fi muni , wannan karon dan jarida daya ne aka samu yake daure a lokacin da muke hada rahoton wannan kidaya. Dan jaridan da aka daure an sake shi bayan an ba da belin sa baya 1 ga Disemba. Sai dai kuma mahukunta sun tsare sama da ‘yan jarida 60 na tsawon lokaci ba tare da wani dalili ba tun da aka fara yakin basasa a kasar a 2020. Abinda ke faruwa shine rikicin na da alaka da yada labaran da ba haka, da kuma labaran karya da kuma kai-komo da ake samu wajen rashin fahimtar bayanai da ake yadawa a shafukan sada zumunta na yanar gizo. Akalla ‘yan jarida biyar ne ake tsare da su a birnin Mekelle da ke karkashin ikon ‘yan tawayen Tigray. Ba a sanya su cikin ƙidayar CPJ ba saboda wasu ne da ban yan bindiga da hakan ke nuni da irin hadarin dake tattare da dauko labarai a yankunan da ake fama da tashin hankali.
A Rwanda ‘yan jarida uku da ke gidan yari sun buga ayyukan su ne a shafin YouTube, saboda gaba daya gwamnati ta dakile sauran hanyoyin yada labarai da aka saba da su wasu kuma ta saka musu iso akai matuka. Mutum biyu cikin wadannan ‘yan jarida , Aimable Karasira da Dieudonne Niyonsenga ( wanda aka sani da Hassan Cyuma) dukkan su an rika gallaza musu azaba a inda suke daure.
YANKIN LATIN AMURKA
Karancin adadin ‘yan jaridar da aka daure – biyu a Nicaragua, daya a Cuba, daya kuma a Guatemala – nuni cewa lallai na samun ci gaba da tabarbarewar ‘yancin ‘yan jarida a yankin. Shekarar 2022 ta kasance shekara mafi muni musamman ga ‘yan jarida a Mexico da Haiti, kuma kasashe da dama sun amince da sabbin dokoki dake bada damar a hukunta duk wanda yayi wani furici da bai kwanta wa mahukunta ba da kuma labarai.
A Guatemala, babban kamun da aka yi wa José Rubén Zamora, ya aike da sako mai ban tsoro ga ‘yan jarida, musamman masu yin zurfin bincike da masu zaman kansu, gabanin zaben badi da kuma ci gaba da murkushe masu gabatar da kara, da alkalai, da ‘yan jarida wadanda a baya suka gabatar da kararrakin cin hanci da rashawa. Zamora, wanda ya kafa kuma shugaban elPeriódico, yana fuskantar tuhumar satar da harkallar kudaden haram, cin zarafi, da kuma daure wa harkalla gindi, tuhume-tuhumen da ake gani a matsayin ramuwar gayya ga rahoton elPeriódico kan zargin cin hanci da rashawa da ya shafi Shugaba Alejandro Giammattei da Babban Lauyan Gwamnati Consuelo Porras. ElPeriódico ya dakatar da buga labarai a jarida ranar 1 ga Disamba, yana mai cewa an tilasta masa yin hakan ne bayan “kwanaki 120 da aka yi ana tirsasa da matsi da kuma takura kan ‘yan cinsa a siyasance da tattalin arziki.
A Nicaragua, hare-hare, kame, da barazanar dauri sun tilastawa kusan dukkanin ‘yan jarida masu zaman kansu na kasar yin hijira ko kuma barin aikinsu; Irin wannan yanayi yana faruwa a Cuba.
GABAS TA TSAKIYA DA AREWACIN AFIRKA
Masar da Saudiyya na ci gaba da zama a cikin kasashe 10 dake kan gaba da ke daure ‘yan jarida a gidajen yari. A Egypt kawai akwai yan jarida 21 dake daure a kurkuku sai kuma 11 dake daure a Saudiyya.
Masar, a karkashin matsin lamba daga Amurka da Majalisar Tarayyar Turai kan yadda take ta ke ‘yancin dan Adam, ta hada da wasu ‘yan jarida cikin fursunonin da ta saki a cikin wannan shekara, amma ta ci gaba da tsare wasu – daga cikinsu akwai edita Ahmed Fayez saboda ya wallafa a Facebook cewa hukumomin gidan yari suna ciyar da dan jarida Alaa Abdelfattah ta karfin tsiya dole a lokacin da yake yajin kin cin abinci na tsawon lokaci.
Ko da yake an samu raguwar yawan wadanda aka tsare daga yawan na bara, da Masar ke da mutum 25 da Saudi Arabiya na da mutum 14, sannan kuma kafofin yada labarai na ci gaba da fuskantar matsin lamba kuma, a bangaren Saudiyya, har yanzu suna fuskantar mummunar fargaba kan kisan dan jarida Jamal Khashoggi.
A Qatar, yayin da babu wani dan jarida da aka daure a dalilin aikinsu a lokacin da kungiyar ta CPJ ta yi wannan kididdiga na kidaya, aikin dauko rahotannin gasar cin kofin duniya da irin matakan da ak saka ya nuna yadda kasar ke da tsauraran dokoki kan aikin yada labarai.
NAHIYAR TURAI DA TSAKIYAR ASIA
Rasha ta kafa sabbin dokoki don hana yada labarai kowacce iri game da yakin da take yi da Ukraine, ciki har da dakatar da kiran rikici a matsayin yaki, sun toshe sauran kafofin yada labarai masu zaman kansu na kasar. Mafi yawa daga cikin ‘yan jaridun Rasha sun guje wa ɗauri ta hanyar tserewa zuwa gudun hijira. Daga cikin mutane 19 da aka sani suna hannun Rasha, da dama na fuskantar hukuncin daurin shekaru 10 bisa zargin yada “labaran karya.”
Tajikistan ta daure ‘yan jarida shida, wanda hakan ya sa ta ke a kan gaba wajen daure ‘yan jarida a tsakiyar Asiya. Fursunonin, wadanda kame su ya biyo bayan mumunar murkushewar da gwamnati ta yi a yankin Gorno-Badakhshan da ke fama da rikici, an gurfanar da su ne a boye a wuraren da ake tsare da su, ba kotuna ba, kuma an yanke musu hukuncin dauri na tsawon lokaci a gidan yari da kuma zargin ana azabtar da su.
Kasar Geogia da ta yi fice wajen mutunta dimokuradiyya a kasar kafin yanzu, ta tsinduma cikin rahoton bayanan kididdigar kidayar CPJ a karon farko, bayan an daure ‘Yar jarida mai gabartar da shirye-shiryen Talabijin na tsawon shekaru 3 da rabi a cikin watan Mayun 2022.
Arlene Getz ita ce babban direktan kuma edita na Kwamitin Kare ‘Yancin ‘Yan jarida. Tana zaune a New York, kasar Amurka, ta yi aikin aiko da labarai daga Nahiyar Afrika. Turai, Asia da Gabas ta tsakiya a matsayin wakiliyar dauko labarai, edita sannan babban edita a jaridar Newsweek. Kafin ta fara aiki da CPJ ta shafe shekaru tara a Reuters inda ta yi aiki a matsayin babban edita mai kula da ayyukan da ya shafi labarai daga sassan na duniya.
HANYOYIN DA AKA BI WAJEN AIKIN WANNAN KIDIDDIGA ( KIDAYA)
Kididdigar Kidayar gidajen yarin da aka yi ya shafi ‘yan jarida ne kawai da gwamnati ta tsare sannan ba a hada da wadanda suka bace ko kuma wadanda ba gwamnati ne ke tsare da su ba, wato suna hannun ‘yan bindiga. An saka su a bangaren ko dai sun “bace” ko kuma an yi “garkuwa” da su.
CPJ ta bayyana ‘yan jarida a matsayin mutanen da ke dauko labarai da yadawa ko sharhi kan al’amuran jama’a a kowace kafofin watsa labarai, ciki har da bugawa a jarida, hotuna, rediyo, talabijin, da kuma a yanar gizo. A kidayar gidan yari na shekara-shekara, CPJ ta saka ‘yan jarida ne kawai wadanda ta tabbatar an daure su bisa dalilin ayyukan aikin sun a jarida.
Duka sunayen da CPJ ta bayyana a cikin rahoton na wadanda ke tsare ne zuwa karfe 12:01 na safiyar ranar 1 ga Disamba, 2022. Rahoton bai hada da yawancin ‘yan jarida da aka daure aka kuma sake su a tsakanin shekaran ba; ana kuma iya samun labarai game da duk rahoton a shafin mu a http://cpj-preprod.go-vip.net. Sunayen ‘Yan jaridan dake daure za su ci gaba da kasancewa a cikin jerin sunayen wadanda ke daure dake kundin mu na CPJ har sai kungiyar ta samu tabbacin cewa an sake su ko kuma sun mutu a tsare tukunna.
Wadanda suka hada wannan rahoto na kididdigar kidaya na CPJ da aka yi sun hada Beh Lih Yi, Anna Brakha, Shawn Crispin, Doja Daoud, Sonali Dhawan, Assane Diagne, Jan-Albert Hootsen, Iris Hsu, Nick Lewis, Kunal Majumder, Sherif Mansour, Scott Mayemba, Attila Mong, Muthoki Mumo, Renata Neder, Özgür Ögret, Evelyn Okakwu, Angela Quintal, Waliullah Rahmani, Yeganeh Rezaian, Justin Shilad, Jonathan Rozen, Gulnoza Said, Natalie Southwick, da Dánae Vílchez
Wadanda suka tantance labaran sun hada da Arlene Getz, Jennifer Dunham, Naomi Zeveloff, Erik Crouch, Sarah Spicer, Madeline Earp, Suzannah Gonzales, and Tom Barkley